Haifuwar Yesu

We are getting closer to Christmas, the day Christians celebrate the birth of Jesus. Here is a simplified Hausa version of the story of Jesus’ birth, as it is written in the Bible in the gospel of Luke, chapter 2 :

1 A kwanakin nan, Kaisar Augustas ya ba da umarni a ƙirga dukan mutanen da suke a ƙarƙashin mulkin Roma. 2 Wannan shi ne ƙirga na farko wanda aka yi lokacin da Kiriniyus yake mulkin ƙasar Suriya. 3 Dukan mutane suka koma garuruwansu domin a ƙirga su.

4 Yusufu ma ya bar garin Nazarat a cikin Galili ya je birnin Baitalami a cikin Yahudiya, wato, garin da aka haifi sarki Dauda ke nan. Yusufu ya je can domin shi daga dangin Dauda ne. 5 Ya tafi tare da Maryamu da aka yi alkawari zai aura, domin a ƙirga su tare. Lokacin nan kuwa tana da ciki.

6 Da suna can Baitalami, sai kwanakin haihuwarta suka yi. 7 Ta haifi ɗanta na fari, ta rufe shi da zanen goyo, ta kuma kwantar da shi a abin da ake ba wa dabbobi abinci a ciki, domin ba su sami ɗaki a masaukin ba.

8 A wannan gefen ƙasar kuwa, akwai waɗansu masu kiwo suna kwana a fili, suna lura da dabbobinsu da dare. 9 Ba labari sai ga mala’ikan Ubangiji ya bayyana gare su, kuma ɗaukakar Allah ta haskaka su. Sai suka ji tsoro sosai. 10 Amma mala’ikan ya ce musu, “Kada ku ji tsoro! Gama na zo muku da Labari Mai Daɗi, wanda zai sa dukan mutane su yi farin ciki sosai.11 A yau ɗin nan, a cikin birnin Dawuda, an haifa muku Mai Ceto, Almasihu Ubangiji! 12 Wannan ne zai zama muku alama, za ku samu an rufe yaron da zanen goyo, an kuma kwantar da shi a abin da ake ba wa dabbobi abinci a ciki.”

13 Ba labari sai ga ƙungiyar mala’iku daga sama sun bayyana tare da mala’ika na farin, suna yabon Allah suna cewa, 14 “Ɗaukaka ga Allah a can cikin sama! A duniya bari salama ta kasance tare da waɗanda Allah yake jin daɗinsu!”

15 Da mala’ikun suka rabu da su suka koma sama, sai masu kiwon suka ce wa junansu, “Bari mu je Baitalami mu ga abin nan da ya faru, da Ubangiji ya gaya mana.”

16 Sai suka tafi da sauri, suka ga Maryamu da Yusufu, suka kuma ga yaron yana kwance a abin da ake ba wa dabbobi abinci a ciki. 17 Da masu kiwon suka gan shi sai suka ba da labarin abin da mala’ikan ya faɗa musu a kan yaron. 18 Dukan mutanen da suka ji wannan labari, sai suka yi ta riƙe baki suna mamakin abin da masu kiwon nan suka ce. 19 Maryamu kuwa ta riƙe dukan waɗannan abubuwa, tana tunaninsu a zuciyarta. 20 Masu kiwon kuma suka koma, suna ta yin waƙoƙin yabon Allah, saboda dukan abin da suka ji, suka kuma gani. Kome ya faru kuwa kamar dai yadda mala’ikan ya faɗa musu.

(taken from: Littafin sabon alkawari, The New Testament in Hausa Common Language. Apapa, Lagos: Bible Society of Nigeria)

If you prefer to listen to the story, visit the Hausa section of Talking Bibles International.

One thought on “Haifuwar Yesu”

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s