Ba sarki sai Allah

A month ago, I wrote a blog post about Hausa texts found in the Internet Archive. The copyright of these texts has expired because the author/editor/compiler of the texts has died more than 70 years ago. I promised to edit some of the old Hausa texts and publish them on this blog. So, here is the first one. I have changed only a few of the words to Standard (i.e. Kano) Hausa. Probably there are still some mistakes left. Please forgive my ignorance.

Ba sarki sai Allah

In an zo fadanci, an ce „Ran sarki ya daɗe.“ Sai wani mutum ya ce „Ba sarki sai Allah.“ Kullum kullum haka, sai sarki ya ji fushi da shi, sai ya kawo zobe biyu azurfa, ya ba shi ajiya, in ji sarki. Ya ce za’a gama da shi. Ba-Sarki-Sai-Allah sai ya ɗauki zobe biyu, ya zuba a ƙafon rago, sai ya ba matanshi ajiya, shi, Ba-Sarki-Sai-Allah.
Sai da aka kwana biyar, sai sarki ya ce „Ba-Sarki-Sai-Allah, zan aike ka wani ƙauye.“ Ya ce „To.“ Da ya aike shi, ya ce „A ce da talakawa su zo ginin gari.“ Da ya tafi, sai sarki ya ce „A je wurin matan Ba-Sarki-Sai-Allah,“ ya ce „A ba ta zambar ɗari, a ba ta zane ɗari, alfuta ɗari, ita kuma ta ba sarki abin da Ba-Sarki-Sai-Allah ya ba ta ajiya.“ Sai ta ce „To,“ sai ta kawo ƙafo, ta ba su. Sarki ya tafi, ya buɗe, ya duba, ya ga zobenshi a ciki. Sai sarki ya mayar a cikin ƙafo, ya dwaɗe, ya ce „A ɗauka, a saka a wani taugi da ba shi ƙonewa.“ Da zuwa, da aka je tafki, aka jifa ƙafo, sai wani ƙaton kifi ya haɗiye.
Sai ran nan, sai Ba-Sarki-Sai-Allah ya dawo daga tafiya. Da ya dawo daga tafiya, sai mutanen gari suka ce za’a yi su a tafkin nan. Da aka je, sai ɗan Ba-Sarki-Sai-Allah ya kama ƙaton kifin nan sai ya zo ina fidi, ina fidi, sai wuƙa ya taba ƙafo keras ! Sai ya ce „Opp, da wani abu a cikin kifi.“ Sai Ba-Sarki-Sai-Allah ya ce „Minene ? „Sai ɗan ya ce „Ai, da wani ƙafo a ciki.“ Sai ya ce „Ɗauko mu gani. „Sai ya ɗauka, sai ya ba uban. Sai ya buɗe ƙafo, ya duba, sai ya ga zoben sarki da ya ba shi ajiya. Sai ya ce „Ba sarki sai Allah kuwa.“
Sun gama feɗen kifi ke nan, sai manzon sarki ya zo, ya ce „Ba-Sarki-Sai-Allah, in ka sha ruwa sarki yana kiranka.“Sai ya ce „To.“ Da manzon ya tafi, sai ya ce da matansa „Ina ajiya da na ba ki?“ Sai ta ce „A, ni, ban sani ba, ko ɓera ta ɗauko shi.“ Sai ya ce „Ba sarki sai Allah.“
Da ya sha ruwa, sai ya kama hanyan fada. Da ya je, ya zauna. Da ya zauna, fadawa suka ce „Ran sarki ya daɗe.“ Sai ya ce „Ba sarki sai Allah.“ Sai sarki ya ce duk fadawa su yi shiru, za’a yi magana da Ba-Sarki-Sai-Allah. Sai ya ce „Ba-Sarki-Sai-Allah.“ Ya ce „I.“ Ya ce „Ina son ajiya na wurinka yanzu-yanzu.“ Sai dogarawa suka tashi, suka tsaye a kanshi, in ba ya ba da ajiyan nan na sarki za’a ɗauke shi a tsiri.
Sai Ba-Sarki-Sai-Allah, sai ya sa hannu a aljifu, sai ya ɗauke ƙafo, ya miƙa ma sarki. Sai sarki ya buɗe ƙafo, ya ga zobenshi. Sai ya ce „Tabbas ba sarki sai Allah.“ Sai fadawa suka ɗauka Ba-Sarki-Sai-Allah, sai sarki ya ɗibi mashi rabin gari ya ba shi.

(First published in: Tremearne, A. J. N. Hausa folk tales.  London 1914, p. 51f.)

3 thoughts on “Ba sarki sai Allah”

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out / Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out / Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out / Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out / Change )

Connecting to %s