Tag Archives: Boko Haram

Press Release on Boko Haram

The Permanent Committee of Mega-Chad, an international network concerned with multidisciplinary research on the history and evolution of societies in the Lake Chad basin, has recently issued a public statement denouncing the violent activities of Boko Haram. The statement, with accompanying comments, can be found on the Méga-Tchad Blog.

The communiqué has also been translated into Hausa:

Bayani ga Yan Jaridu

Haɗakar rassan bincike ta ‘Mega-Tchad’ [www.megatchad.net] wata babbar mahaɗa ce ta manyan malamai daga ƙasashen duniya dabam-dabam da masana da masu bincike akan ɓangarorin rayuwar al’ummar da ke zaune a zagayen tafkin Chadi. An kafa wannan haɗaka shekaru 30 da suka gabata, kuma a halin yanzu tana da membobi kimanin 500.

Shugabannin wannan haɗakar suna Allah wadai da irin ayyukan ta’addancin da ’yan ƙungiyar Boko Haram ke gudanarwa tun ba a yankin Borno ba, wanda ya yi sanadiyyar tarwatsa matsugunai da hallakar mutane da dama tare da hasarar dukiyoyi, da kuma danne hakkin jama’ar yankin. Manufar waɗannan miyagun mutane, ’yan Boko Haram, shi ne amfani da addini domin cimma manufofin siyasa ta hanyar rusa tsarin doka da oda domin samun damar ci gaba da gudanar da munanan ayyukansu na ta’addanci a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Ayyukan ta’addanci da wannan ƙungiya ta Boko Haram ke aiwatarwa na bazuwa zuwa maƙwabtan ƙasashe kamar su Kamaru, Chadi da kuma Jamhuriyar Nijar. Ganin kuma damina na ƙaratowa, ana fargabar cewa wannan hargitsi na Boko Haram zai hana gudanar da ayyukan noma kamar yadda aka saba. Hakan kan iya jefa ɗaukacin yankin cikin matsananciyar yunwa. A yanzu haka dubban yara a yankin na zaune a gida babu zuwa makaranta, jami’o’in da ke cikin yankin ba sa iya gudanar da ayyukansu a cikin kwanciyar hankali, kazalika ayyukan masu nazarce-nazarce daga sassan duniya akan ci-gaban yankin sun tsaya. Haka kuma mata ba su da ikon fita waje saboda tsoron faɗa wa hannun ’yan ta’adda. Ɗaruruwan iyaye na cike da baƙin ciki da alhinin halin da ’ya’yansu mata ke ciki waɗanda ’yan ta’adda suka sace.

Akan haka, kwamitin ƙoli na Mega-Tchad na kira da babbar murya ga hukumomin addinin musulunci da su la’anci wannan mummunar aƙida wacce ta saɓa wa koyarwar addinin, la’anta mai tsanani. Haka kuma, kwamitin na roƙon mahukunta da su tashi tsaye wurin yaƙi da wannan ɗabi’ar ta’addanci, wadda ke faruwa a tsakanin iyakokin ƙasashen da ke cikin yankin tafkin Chadi, domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a ɗaukacinyankin.

[The Hausa translation was prepared under the direction of Professor Paul Newman and Dr. Roxana Newman]